ABNA: A jawabin da ya gabatar a yau Asabar, ya yi ishara da jawabin jagoran juyin musulu nci mai cike da hikima wanda ya yi jinjina akan wadanda su ka kera jirgin bayar da horo na “kauthar”, sannan ya kara da cewa; Jawabin yana kara cusa fata a cikin zukatan masana da sauran al’ummar Iran.
Har ila yau, ministan tsaron na Iran ya bayyana nasarorin da aka samu na kere-kere ta fuskar tsaro a cikin Iran daga ciki hadda makamin “Babar 373” na bayar da kariya ta sararin samaniya, da sauran makamai masu linazami samfurorin Cruise da Balastic da jirgin ruwa na yaki mai ninkaya a karkashin ruwa.
342/